www.NaijaBasic.Com

HOME | MUSIC | VIDEO | DJ MIX | ALBUME!


 
Are You A Upcoming Artist ? Do You Want Post Song / Video On Naijabasic.com ? Reach us At Click Here 

« | »

bara zamu hana ba almajirci bah BUHARI

Posted by on Jun 30, 2019.   Under: E-News ,

DOWNLOAD

A wata hira da ya yi da wakilinmu Ishaq Khalid, Malam Garba Shehu, ya ce, gwamnatin Muhammadu Buhari na son ganin ta tsaftace harkar almajirci a arewacin kasar ta yadda za a zauna da masu ruwa da tsaki kan al’amarin domin lalubo bakin zare. Latsa alamar lasifikar da ke sama domin jin hirar da Ishaq Khalid ya yi da Garba Shehu TALLA Wannan batun dai ya ja hankalin ‘yan Najeriya a makonnin da suka wuce, inda a wata sanarwa da Malam Garba Shehun ya fitar, Shugaba Buhari ya bayar da tabbas cewa gwamnatinsa za ta dauki matakin hana bara amma fa ba a nan kusa ba. Kafin sanarwar, sai da Shugaba Buhari ya nanata aniyarsa na ganin dukkanin yara ‘yan Najeriya sun samu ilimin da ya dace da su, inda ya ce zai dauki matakan magance hana kananan yara zuwa makaranta
A ‘yan makonnin da suka gabata ne dai Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya fitar da alkaluman da ke nuna cewa kimanin kananan yara miliyan takwas ba sa makaranta a jihohi 10 na Najeriya. Asusun ya kara da cewa yaran dukkaninsu daga jihohin arewa suke: Bauchi Niger Katsina Kano Sokoto Zamfara Kebbi Gombe Adamawa Taraba. Ana ganin rahoton Asusun na UNICEF na daga cikin abubuwan da suka yi tasiri kan yunkurin daukar matakin da Shugaba Buhari ya ce zai yi wajen ganin an magance matsalar rashin karatun yara a kasar. Me jihohi ke yi kan almajirci? Za a iya cewa batun almajirci yana ci wa jihohin arewacin kasar tuwo a kwarya, ganin cewa duk lokacin da aka fito da wasu alkaluma da ke nuna koma-bayan karatun yara, jihohin ne ke kunyata. A makon da ya gabata Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ja kunnen mahaifan da ke tura ‘ya’yansu almajirci ko kuma bara maimakon makaranta, inda har ya ba da umarnin a kama yaran da mahaifan na su. Shi ma Sarkin Kanon, Muhammadu Sanusi na biyu ya shaida wa ‘yan majalisar jihar da suka ziyarce shi a fadarsa, cewa zai aiko da kudurin doka da zai tilasta wa iyaye kai yaransu makarantun boko. Da zarar majalisar ta amince da kudirin ya zama doka, to duk iyayen da aka samu da laifin kin aika yaransu makaranta za su gurfana ne a gaban kuliya. Ko a baya ma dai jihar ta Kano ta yi dokokin hana bara da suka tanadi kama almajiri da malaminsu, amma har yanzu matsalar ba ta ragu ba maimakon haka ma ƙara gaba-gaba take yi. An dai sha gudanar da bincike da nazarce-nazarce da dama gami da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar bara, musamman a arewacin Najeriya. A 2014 wani kwamitin wasu fitattun mutane da suka shafe wata takwas suna yi wa gwamnonin arewa nazari kan wasu matsaloli musamman na bara, sun gabatar da rahoto kan yadda za a magance su. Sai dai sama da shekara biyar da mika wa gwamnonin wannan rahoto, za a iya cewa ba a ga sauyi ba. Mene ne almajirci? Yanayi ne da iyaye kan tura yaransu zuwa ga wani malami domin koyar da su karatun alkur’ani, a wurin da ake kira makarantar allo. A mafi yawan lokaci, malamin da yaran kan yin nesa da garuruwansu, inda suke zuwa wasu birane domin samun sukunin karatun. Kusan za a iya cewa kadan ne daga cikin mahaifan yaran kan bai wa malamin abincin da yaran na su za su ci a tsawon zaman da za su yi da shi. Mafi yawancin yaran kan fita bara kan tituna da gidaje domin neman abin da za su ci da ma neman kudin bukatunsu na yau da kullum.

Add us for Music Promotion, Share Your Story and Advertsing your Products / Brands Email: [email protected] / WHATSAPP: 08025077766 / 0705***
AD

Tags:


ADVERTISE ON NAIJABASIC

Have Something Interesting Informative you want us to Post on NaijaBasic.com ? Send to [email protected]

No Responses Yet

Leave a Reply

« | »