www.NaijaBasic.Com

HOME | MUSIC | VIDEO | DJ MIX | ALBUME!


 
Are You A Upcoming Artist ? Do You Want Post Song / Video On Naijabasic.com ? Reach us At Click Here 

« | »

News: Harin libya Dabbancine Buhari

Posted by on Jul 3, 2019.   Under: E-News ,

DOWNLOAD

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum 40 suka mutu bayan 80 suka samu raunika a harin bam din wanda ya tarwatse a wata cibiya da ke wata unguwa a gabashin birnin Tripoli. ‘Yan Najeriya da dama ne suka rasa rayukansu a harin da aka kai kan ‘yan ci-rani, wadanda ke hankoron tsallakawa zuwa nahiyar Turai domin samun rayuwa mayalwaciya. A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, shugaban ya ce akwai bukatar a yi bincike na musamman kan harin wanda aka kai shi ta sama. “Hari ta sama da aka kai kan sansanin ‘yan ci-rani a Tripoli dabbanci ne mai cike da keta da kuma rashin tausayi. Lallai ne a yi bincike a gurfanar da wadanda suka aikata shi a gaban kotu.” Tarzoma da rarrabuwar kai sun daidaita Libya tun bayan hambarar da kuma kashe Shugaba Muammar Gaddafi a shekarar 2011. Osama Ali, mai magana ne da yawun hukumomin ba da agaji ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wani hari ne daga Tajoura kai tsaye ya fada wa wata rumfa da ake tsare ‘yan ci-rani 120. Ya ce mai yiwuwa ne mamatan su fi 40 domin kuwa kididdigar mutanen da aka kashe din ta farko- farko ce. Cibiyoyin tsare ‘yan ci-ranin dai sun shiga tsaka mai wuya.

Gwamnatin National Accord mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wadda Fira minista Fayez ai Serra ke jagoranta ta zargi dakarun Libyan National Army da kai wannan hari na wayewar garin ranar Laraba. Mayakan karkashin jagorancin Khalifa Haftar na fada ne da dakarun gwamnatin da kasashen duniya ke marawa baya a yankin da harin ya auku.

A ranar Litinin ne ta sanar da cewa za ta fara kai hare-hare ta sama cikin birnin Tripoli bayan hanyoyin da aka saba da su sun faskara. Sai dai mai magana da yawun mayakan ya musanta cewa dakarunsu ne suka far wa cibiyar tsare mutanen.

Add us for Music Promotion, Share Your Story and Advertsing your Products / Brands Email: [email protected] / WHATSAPP: 08025077766 / 0705***
AD

Tags: ,


ADVERTISE ON NAIJABASIC

Have Something Interesting Informative you want us to Post on NaijaBasic.com ? Send to [email protected]

No Responses Yet

Leave a Reply

« | »